MURNAR AURE by David Yohanna Jankoli — Lyrics

David Yohanna Jankoli Hausa Wedding Hymns Celebrations Solfa notation

Full Lyrics

VERSE 1 Mu na murna yau, murna, murnar aure. Ku zo mu yi murna yau domin wannan aure. Auren ( ) a yau da ( ) Allah ya shirya, ba mai rabawa. Sam! Sam!! Sam!!! VERSE 2 Mu na murna yau domin wannan aure. Ga mutane sun zo su shaida auren Krista, aure ne mai tsaki. Allah ya shirya, ba mai rabawa. Sam! Sam!! Sam!!! VERSE 3 Ga Amarya pes pes ta na murna. Ga Ango ma ya na murna, dukan shaidu su ma su na murna. Allah ya shirya, ba mai rabawa. Sam! Sam!! Sam!!! PART ENTRY Allah ya ba ku ciki da goyo. Ku yi addu'a. Ku yi zaman ƙauna. Mun zo mu yi murna. Kullum ku yi ƙauna. Ku rayu tare. Ku yi zaman ƙauna. Allah ya ba ku ciki da goyo. Allah ya shirya, ba mai rabawa. Sam! Sam!! Sam!!! VIVACE Mu na murna domin wannan aure a yau, auren ( ) da ( ). Mu na da murna yau domin auren nan. Mu na da murna Allah ya haɗa su.

Download the sheet music

MURNAR AURE

MURNAR AURE

By David Yohanna Jankoli
Solfa
Hausa
2 pages
2 Downloads
Wedding Hymns Celebrations
1 0

More lyrics you may want