Full Lyrics
VERSE 1
Lokaci ya riga ya yi sai mu falka daga barci mun dai san
Irin zamanin da muke a cikinsa yau dare fa ya kure
Sai mu watsar da ayyukan duhu mu juyo ga Ubangiji
Mu mika zukatan mu duk, gama lokaci yayi sai
VERSE 2
Mu taf'yar da alamuran mu yadda ya dace mu yi ba a cikin
Shashanci da buguwa ko faskanci ba amma mu bi halin
Ubangiji Yesu Almasihu domin shine hanyar da zai
Kaiku zuwa ga nasara gama lokaci yayi sai
VERSE 3
Masu bi lokaci yayi sai mu falka daga barci mu fara
Shiri don ceton nan yana kurkusa damu gari fa ya kusan
Wayeye gama lokaci yayi mu tuba, tuba na gaskiya
Don karmu rasa ceto gama lokaci yayi sai
REFRAIN
Mu falka daga barci
Gama daren nan ya kare gashi gari zai waye
Lokaci ya riga ya yi sai mu falka daga barci
Mu juyo ga Ubangiji mu mika zukatan mu duk
KU JUYO WURIN UBANGIJI TUN YANA KUSA
SOPRANO
Ku juyo wurin Ubangiji ku yi addu'a a gare shi
ALL CHOIR
Tun yanzu da yake nan kusa
Tun yanzu da yake nan kusa
Ku juyo, ku juyo
Ku juyo kada ku rasa shi