Full Lyrics
VERSE 1
Da na zauna cikin zunubi,
Ba na kula da Ubangiji,
Ko mutuwa wadda shi ya yi
domina kan gic'ye.
VERSE 2
Na ji zancen ladan zunubi,
Tsoron mutuwa ta kama ni.
Sai na roki jinkan maiceto,
domina kan gic'ye.
VERSE 3
Na yi murna marar Iyaka
Tunda Yesu Ya yi ceto na,
Ina rera wakar yabonsa,
kullum ba fasawa.
VERSE 4
Nufina in Kawo daraja
Wurin Yesu Ubangiji na,
Sa'annan in dubi fuskarsa,
yau da har abada.
REFRAIN
Jinkan Yesu,
Ya yi mini,
Aikin gafara,
Kayan laifi na ya dauka
k'wa kan gic'ye.