Full Lyrics
VERSE 1
Yesu Kristi yau ya tashi, ba zai sake mutuwa ba
a ka sa shi kabarin sa, yau ya fashe sarkan sa;
Almasihu ba ya nan tashin sa ya tabbata,
Jikin sa mai tsarki ne, ba zai rube ba dadai.
VERSE 2
Yesu Kristi yau ya tashi shaidar nasara ne fa kai
cikin sama wurin Allah, yau har abada mai rai!
Shi mai daukar fansan mu ya isa mu yabe shi,
radadin sa ya wuce ya isa mu yabe shi.
VERSE 3
Jama'ar Yesu, ku tuna haihuwar sa da mutuwa;
rundunan sama, ku duba, ga mutun mai nasara;
Shi kadai ma jiki ne cikin sama fa yanzu,
cikin jiki mun sami daraja har abada.
CHORUS
Yesu Kristi yau ya tashi, ba zai sake mutuwa ba,
zo, mutane, raira waka, shi ne sarkin sarakuna;
tsoron mutuwa ya kare, wannan fa mun gaskata,
ikon mutuwa banza ne, ya tashi, yara da rai.