Full Lyrics
VERSE 1
Yesu ne garkuwan mu a kullayomi,
Yana nan da mu ba za mu taɓa jijjigu ba,
Yana kiyaye mu a cikin kowace yanayi.
Muna yanga da sunan Yesu kayan adon mu.
VERSE 2
Ko muna shan wahala a kullayomi,
Muna da Uba shi zai rike mu da hannun sa,
Shine masoyin mu, wurin sa ne mu ke dogara.
Muna yanga da sunan Yesu kayan adon mu.
VERSE 3
Ubangiji na da kyau a kullayomi,
Ba ya sakewa, kaunar sa madawwamiya ce,
Alherin sa na nan domin ya rike mu ko yaushe.
Muna yanga da sunan Yesu kayan adon mu.
CHORUS
Yesu ne garkuwan mu masu bi,
A karkashin inuwan sa za mu huta,
Wurin zaman mu ne kullum.
Mun jingina a wurin sa, mun jingina,
Mun jingina a wurin sa, mun jingina ko yaushe.