Full Lyrics
VERSE 1
Yabo ga Allah domin alherin sa da jinkan sa da yake yi mana,
mu daukaka shi da kalmomin yabo mu yabe shi don ya Isa yabo.
VERSE 2
Tun mun fadi ya kauna ce mu harya aiko da Dansa Yesu domin mu,
ya bada ransa hadaya duk domin kada mu rasa shiga mulkin sa.
VERSE 3
Can kan gic'ye ya sha wahala domin mu sami rai madauwami a yau,
an gic'ye shi ya sha hazaba domin mu sami ceto daga mutuwa.
CHORUS
Yabo ya tabbata ga Allahnmu don kaunar sa
da jinkan sa
Yabo ya tabbata ga Allahnmu don kaunar sa
da jinkan sa