Full Lyrics
CHORUS
Domin jagorancin ka Uba mun gode,
Kai ke kiyaye mu kullum Uba mun gode,
Domin alherin ka Uba mun gode,
Domin bishewar ka Uba mun gode,
Mun gode, Uba mun gode,
Mun gode, mun gode.
VERSE 1
Shekaru da dama oh! na yakin bishara,
'Ya'yanki suna alfahari da hanyar da kike bi cikin hasken Kristi.
E! kofar ki a bude take,
E! kofar ki a bude take,
Ga wadanda suka karbi Yesu,
Ga wadanda suka karbi Yesu.
VERSE 2
Kin shaida tauraron da ta nuna hanya ga shehunna:
Godiya tabbata ga Allah.
Hasken nan ta mamaye ta fita kuma daga duhu:
Godiya tabbata ga Allah.
Hakika a cikin ruwan sama da mugun yanayi:
Godiya tabbata ga Allah.
Kin rayu kin jagoranci hidimar Krista ba gajiya:
Godiya tabbata ga Allah.
Mu sojojin Yesu ne E! masu yakin bisharan Yesu,
'Ya'yanki sun girma sun zama mashaidun Yesu Kristi.
Ba domin karfin mu ko iyawa ba
Mu ka sami wannan nasaran a yau
Wannan alherin Allah ne,
Wannan alherin Allah ne.