Full Lyrics
VERSE 1
Sunan Yesu ne mafi daukaka; cikin dukan sunaye.
Babu suna wanda ya isa ceton mu sai shi kadai.
VERSE 2
Cikin sunan nan ake yin addu'a; cikin sa akwai ceto.
Wannan suna ba mai kamarsa, wannan sunan Yesu ne.
VERSE 3
Cikin sunan nan ake samun rai; cikin sa, sai kwanc'yar rai.
Cikin wannan suna ake samun rai na har abada.
VERSE 4
Wannan sunan nan shine gadon mu; shine mafakar Krista.
Wannan suna shine kariyar mu, shine dutsen ceton mu.
CHORUS
Ai sunan nan na da iko
Sunan na da dadin ji
Wannan suna ba mai kamar sa;
Wannan sunan Yesu ne.