Full Lyrics
CHORUS
Wayasani ko Ubangiji (Allah) zai sake nufinsa,
Wayasani ko Ubangiji zai sake nufinsa,
Yasa mana albarka har mu mika masa.
VERSE 1
Hadaya ta gari da tasha koyanzu inji Ubangiji,
Ku juyo wurina da zuc'ya daya da azumi,
Ku yi kuka da makoki ku tsabtace zuciyarku,
Ba tufafinku ba ku juyo wurin Ubangiji,
Shi mai alheri ne ku yi addua a gareshi,
Don shi mai jinkai ne ku juyo wurin Ubangiji.
VERSE 2
Zaya sake nufinsa ku yi addua a gareshi,
Zayasa mana albarka har mu mika masa,
Hadaya ta gari da tasha ku busa kaho a sihiyona,
Ku sa a yi azumi ku kira muhimman taro,
Ku yi addua a gareshi.
PART ENTRY (S.A.T.B)
Allah mai jinkai ne zaya ji kukan mu,
Mai jinkai ne Allahnmu mai jinkai ne,
Mai jinkai ne Allahnmu mai jinkai ne.