Full Lyrics
VERSE 1
Sa'an da an bashe shi ga mutuwa, sai sojan mai mulki suka kai Yesu cikin fadar mai mulki, suka tara dukan kungiyar soja a kan sa.
VERSE 2
Sai suka tube shi suka yafa masa wata jar alkyabba, suka yi wani rawani na kaya suka sama sa a kan sa.
VERSE 3
Suka kuma durkusa a gaban sa suna yi masa ba'a, suna cewa ran ka ya dade sarkin Yahudawa, suka tofa masa yawu.
VERSE 4
Da suka gama yi masa ba'a sai suka yaye masa alkyabbar, suka sa masa nasa tufafin suka tafi da shi su giciye shi.
REFRAIN
Za'a bashe shi a giciye shi, amma bayan kwana uku Yesu zai tashi daga matattu kamar yadda ya fada, zai tashi kamar yadda ya fada.