Full Lyrics
VERSE 1
Ina ne zamu je a yau, domin mu sami salama,
Duniya tana karewa ana ta karkashe Krista,
Oh ya Ubangiji Allah, muna rokon bishewanka,
Kada ka boye fuskanka a garemu.
CHORUS
Yakeyake a ko'ina ba salama kullayaumi,
Sai mutuwa ake ta yi domin sunan Almasihu,
Oh ya Allah ina kake mun bada gaskiya kana nan,
Kada ka yashe mu ba,
Oh muna roko.
VERSE 2
Mun kasa ga darajarka, muna rokon gafararka,
Mu masu zunubi ne muna rokon gafararka yau,
Domin mu sami salama, domin mu sami kwanciyar rai,
Domin mu sami ceton shiga mulkinka.
VERSE 3
Duniya tana karewa, ba salama ga mu Krista,
Muna rokonka ya Allah karfafa bangaskiyarmu,
Ina ne zamu je a yau, domin mu sami salama,
Sai dai wurinka ya Allah muna roko.