Full Lyrics
CHORUS
Mun yabe ka da molo da garaya,
Mun yabe ka da molo da garaya,
da kuje, da sarewa bandiri da Kakaki,
da kuje, da sarewa bandiri da kakaki,
yabo ya tabbata ga Ubangijina,
yabo ya tabbata ga Ubangijina.
VERSE 1
Ku yabi Allah a cikin haikalin sa
ku yabi karfinsa a sama da kasa,
ku yabe Shi saboda manyan abubuwa
wadanda ya aikata,
ku yabi maffificin girmansa.
VERSE 2
Ku yabi Ubangiji dukan ku rayayu,
ku yabi Ubangiji rayayan talakai
yabo ya tabbata ga Ubangijina.