Labarin Rayuwata by Enoch Clement — Lyrics

Enoch Clement Hausa Offertory Hymns Hymns Solfa notation

Full Lyrics

VERSE 1 Idan na tunan da abubuwan da kayi mani, ya Ubangiji Allah na. Idan na tuna da wahalan da ka sha domin na. Oh domin na, Ka ce "Ya kare." Oh domin na, Ya Ubangiji. Sai dai kalma Yabo da godiya, karbe su, ka sa mani albarka. CHORUS Ni zan dauka sunan ka, Ya Ubangiji karbi godiya da yabo, ka sa albarka Uba, karbi godiya ka sa mani albarka. VERSE 2 Akwai lokacin da a rayuwata, Ina bakin cikin ga wahala, da hawaye, Ina kuka. Amma ga shi, ka kubutar da ni, Allah, ka bani salama, ka canza rayuwata daga bakin ciki zuwa farin ciki. Sai dai kalma Yabo da godiya, karbe su, ka sa mani albarka. VERSE 3 Akwai makafai, kuramai, kassasu, da marasa lafiya, Amma ya Ubangiji, ka halicce ni da komai. Ka bani lafiyan jiki, ba bani abinci, ka bani ruwan sha, ka suturar da ni sai dai kalma yabo da godiya, karbe su, ka sa mani albarka. VERSE 4 Ni zan gaya wa abokanai na da makwabta na Ni zan gaya wa abokanai na da makwabta na! labarin abubuwan, abubuwan, abubuwan da kayi, domin na sai dai kalma yabo da godiya, karbe su, ka sa mani albarka.

Download the sheet music

Labarin Rayuwata

Labarin Rayuwata

By Enoch Clement
Solfa
Hausa
5 pages
1 Downloads
Offertory Hymns Hymns
0 0

More lyrics you may want