Full Lyrics
CHORUS
Kuci jikin Sa, kusha jinin Sa abinci ne kyauta,
Shi ya bamu da Kansa domin mu sami ceto na mu, ta
Sabuwar alkawari, ta sabuwar ceto, ta sabuwar hanya.
VERSE 1
Abinci ne mai dadi, abinci ne mai kyau.
Abincin ceto wanda Shi Yesu ya ba wa duniya,
Don watan wata yana mu ma mu nuna wa yan uwa.
VERSE 2
Idan mun ci burodi, mu sha calis na wain,
Jiki da jinin wanda Shi Yesu, ya ba wa duniya,
Don watan wata yana mu ma mu nuna wa yan uwa.
VERSE 3
Musa ido ga Yesu wanda Uba ya aiko,
Domin mu sami wannan salama, ya ba wa duniya,
Don watan wata yana mu ma mu nuna wa yan uwa.
VERSE 4
Idan muna kasawa, idan fa mu na yunwa,
Ga abincin ruhu da Shi Yesu, ya ba wa duniya,
Don watan wata yana mu ma mu nuna wa yan uwa.
VERSE 5
Kuzo wurin Dan Allah, kuzo wurin mai rai,
Ga Dan tunkiya wanda Shi Allah ya ba wa duniya,
Don watan wata yana mu ma mu nuna wa yan uwa.