Full Lyrics
VERSE 1
Gaya wa Yesu duk damuwar ka
Shi zai biya duk bukatar ka.
Yesu Mai tausayi ne zai share hawaye
VERSE 2
Gaya wa Yesu duk radadin ka
Shi zai maganta wahalarka.
Zai ba ka kwanciyar rai da biyan bukata.
VERSE 3
Ko mu na so mu guje zunubi.
Mu yi addu'a Allah yana ji.
Zai ba mu nasaransa ko wani lokaci.
VERSE 4
Mu yi addu'a, shi ne nasara.
Ba addu'a babu nasara.
Addurar bangaskyarka zai kawo nasara.
CHORUS
Masu bi kada mu damu Yesunmu na nan.
Ku zo mu kai wa Yesu duk damuwar mu.
Ya na marmari mu kawo damuwar mu ko
da safe, ko da rana, ko da yamma, ko da dare.
Mu kawo damuwar mu ga Ubangiji.