Full Lyrics
REFRAIN
Daukaka ga Allah a cikin samaniya,
Daukaka ga Allah a cikin samaniya.
VERSE 1
Aduniya kuma salama ga mutane na nufi mai kyau.
Muna yabon ka,
Muna albarkace ka,
Muna yima ka sujada,
Muna daukakar ka,
Muna godiya saboda daukakar ka mai girma.
VERSE 2
Ya Ubangiji Allah, Sarkin Sama,
Allah Uba mai iko duka.
Ya Ubangiji Yesu Almasihu Da makadaici,
Ya Ubangiji Allah Dan tunkiya na Allah,
Dan Uba.
VERSE 3
Kai da kake warda zunuban duniya kayi mana jinkai.
Kai da kake warda zunuban duniya kaji addu'ar mu.
Kai da kake zaune a hannun dama na Uba,
Kayi mana jinkai.
VERSE 4
Domin kai kadai mai tsarki ne,
Kai kadai Ubangiji ne,
Kai kadai ne madaukaki,
Ya Yesu Almasihu,
Tare da Ruhu Mai Tsarki,
Cikin darajar Allah Uba.
Amin, Amin, Amin.