Full Lyrics
A wannan yankin kasar kuwa
Wadansu makiyaya suna kwana a filin Allah,
Wadansu makiyaya suna kwana a filin Allah.
Suna tsaron, suna tsaron garken su;
Iye nanaye, sai ga wani mala'ikan Ubangiji tsaye kusa da su,
Daukakar Ubangiji kuma ta haskaka.
Sai mala'ikan ya ce masu
Kada ku ji tsoro;
Ashi albishir na kawo maku na farin ciki mai yawa;
Wanda zai zama na duk mutane.
Iye nanaye aiye nanaye,
Domin an haifi mana mai ceto;
Iye nanaye, aiye nanaye, an haifi mana mai ceto;
Domin an haifi mana mai ceto;
Iye nanaye aiye nanaye, an haifi mana mai ceto;
Daukakar Ubangiji kuma ta haskaka.
Kada ku ji tsoro;
Ashi albishir na kawo maku na farin ciki mai yawa;
An haifi, an haifi, an haifi,
Iye, iye, nanaye an haifi mana mai ceto;
A birnin Dauda an haifi mana mai ceto.