Full Lyrics
Gata nan gaba nan ku ta zo mu ji ta,
Kunji labarin Isah Almasihu? I mun ji,
Ya zo duniya har mun sami ceto ya tafi Lahira.
Bai yashe abokainsa ba, ya yi mana alkawarin ruhu,
To gashi nan ruhu mai tsarkin ya sauko, ah.
Ya sauko daga Sama Ubangiji mun gode.
Haleluya! Zo mu raira yabo,
Ku zo mu raira, raira yabo.
Ruhu mai tsarki sauko ko ya ruhu sauko,
Ruhun Allah, sauko,
Zo ka bishe mu ruhun Allah, ka sauko ya ruhu.
Ruhu mai tsarki sauko ka bishe mu bayin ka,
Sauko ruhu, ka sauko ruhu,
Ka bishe mu uba da ruhu mai tsarki.
Ya ruhu mai tsarki ruhu ka bishe mu,
Ruhun Allah ka bishe mu,
Ruhu mai tsarki sai ka sauko!
Ya sauko! Ya sauko!
Ruhun Allah ka bishe mu ruhun Allah,
Kamar yarda ka sauko a ranar Fentikos. Haleluya!
Ruhu mai tsarki sauko, yana tare da mu. Haleluya!
Ruhu mai tsarki yana tare da mu.
Alkawari. Haleluya!
Alkawarin Allah i ya cika,
I ya cika zo ku gani lallai ya cika.
I zo ku gani abin farinciki yanuwa,
Ruhu mai tsarki Allah ya ba mu,
Yesu bai yashe mu ba,
To ga ruhun ya sauko,
Alkawarin Yesu Kristi ya cika. Lallai ya cika!
Mai tsarki ya sauko,
Mu yi godiya mu gyara zama,
Aiye mun gode Allah, gyara zama yanuwa,
To ga labarin ceton mu an kawo.
Jama'an Allah, to ga labarin ceton mu an kawo.
Gara ya molo ruhun Ubangiji ne ya ba mu kwazo, kai!
Aiye! To ga labarin ceton mu an kawo.
Yesu ya mutu ya tashi,
Amma bai yashe mu ba ya turo ruhun sa,
Yesu ya turo ruhun Sa mai tsarki!
Mai tsarki!