Full Lyrics
[CHORUS]
Ku zo mu karbi Jikin da jinin Yesu Kristo
domin mu sami rai na har abada.
Jikin da jinin Yesu shine abinci rai,
Abinci zumunci, zumunci abinci Yesu Kristo,
jikin da jinin Yesu Kristo.
Zo mu karbi Yesu.
[SOPRANO SOLO 1]
Ku zo mu je mu karbi da zuciya mai tsarki,
Wannan shine abinci mai bada rai.
Ku zo mu karbi rai.
[VERSE 1]
Ku zo mu karbi albarka,
Ku zo mu sami rahama,
abincinsa yana da kyau,
Abinci Yesu Kristo.
[SOPRANO SOLO 2]
Abinci mai dadi,
Abinci Yesu Kristo,
zamu ci wannan abinci Yesu Kristo.
[SOPRANO SOLO 3]
Mu dogara wa Yesu shine Uba shine mai tsarki,
Mai tsarki, mai tsarki, mai tsarki, mai tsarki,
bari mu dogara Yesu Kristo.
[VERSE 2]
Duk wanda suke ci naman jikina,
a cikina yake zauna,
Yake shan jinina,
ni kuma a cikinsa.