Full Lyrics
CHORUS
Abincin alheri, shine za mu ci.
Shiryaye daga wurin Allah, Oh! abincin alheri za mu ci.
Shiryaye daga wurin Allah, Oh! abincin alheri za mu ci.
VERSE 1
Yesu ya dauki Gurasa
Ya ba mu Ya ce
Wannan shine jikina da za a ba dukan mutane.
Kristi ya dauki koko
Ya ba mu Ya ce
Wannan shine Jinina da za a ba dukan mutane.
VERSE 2
Gurasa da koko da mu karbi
shine Jiki, shine Jinin Yesu.
Duk wanda ya karbi shi a cikin tsarkakiya zuciya
zai sa mu Rai har abada,
zai sa mu Rai har abada.
VERSE 3
Kuzo ku karbe shi,
Kuzo ku karbe Shi, masun bauta.
Yana da dadi,
Zai ba ku Rai,
mai Tsarki, mai Kauna,
mai Jinkai, mai salama.
Kuzo ku karbe shi.