Full Lyrics
REFRAIN
Ya Ubangiji, ka zo don taimako na.
VERSE 1
Na yi ta jiran taimakon Ubangiji,
sa'annan ya kasa kunne gare ni,
ya ji kuka na.
VERSE 2
Ya fisshe ni daga rami mai hatsari,
ya aza ni a kan dutse lafiya lau.
Ya kawar mini da tsoro.
VERSE 3
Ya koya mini raira sabuwar waka
wakar yabon Allahn mu.
Dayawa idan suka ga wannan
zasu tsorata zasu kuma dogara ga Ubangiji.
VERSE 4
Ba ni da karfi ba mataimaki,
ya Allah ka zo wurina da hanzari.
Kai ne mataimakina da mai cetona,
kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji.