Full Lyrics
[CHORUS]
Domin jagorancin ka Uba mun gode.
Kai ke kiyaye mu kullum Uba mun gode.
Domin alherin ka Uba mun gode.
Domin bishewar ka Uba mun gode, mun gode.
Uba mun gode, mun gode.
Uba mun gode, mun gode.
Mun gode.
Shekaru da dama, Oh! Na yakin bishara.
'Ya'yan ki su na alfahari da hanyar da ki ke bi cikin hasken Kristi.
I! Kofar ki a buɗe ta ke.
I! Kofar ki a buɗe ta ke ga waɗanda su ka karɓi Yesu,
ga waɗanda su ka karɓi Yesu.
[VERSE 1]
Kin shaida tauraron da ta nunah hanya ga shehuna;
godiya ta tabbata ga Allah.
[VERSE 2]
Hasken nan ta mamaye, ta fita kuma daga duhu;
godiya ta tabbata ga Allah.
[VERSE 3]
Hakika a cikin ruwan sama da mugun yanayi;
godiya ta tabbata ga Allah.
[VERSE 4]
Kin rayu, kin jagoranci hidimar Krista ba gajiya;
godiya ta tabbata ga Allah.
[CODA]
Mu sojojin Yesu ne.
I! Masu yakin bisharan Yesu.
'Ya'yan ki sun girma sun zama mashaidun Yesu Kristi.
Ba domin karfin mu ko iyawa ba
mu ka samu wannan nasaran a yau,
wannan alherin Allah ne,
wannan alherin Allah ne.