Full Lyrics
REFRAIN
Zo mu je gaban gaba gadi,
Zo mu je wurin Dan tunkiya,
Jininsa da namansa kan Sakarmenti ne mai dadi.
VERSE 1
A daren da aka bashe Yesu,
Da yardarsa ne ya dauki burodi,
Da waina ya mika,
Ya mika ya ba almajiransa a Sakarmenti.
VERSE 2
Ai ni ne gurasa mai rai (Gurasar rai)
Ai ni ne wanda ya sauko (da ya sauko)
Daga gun Uba na sama (sama)
Ni ne mai ba da rai ai Sakarmenti
VERSE 3
Duk wanda ya ci namana (ci namana)
Duk wanda ya sha jinina (sha jinina)
Zai rayu da ni a sama (sama)
A kursiyin Ubana Sakarmenti
VERSE 4
Ya Dan Tunkiya na Allah (Tunkiyan Allah)
Mun durkusa nan gabanka (nan gabanka)
Cika mu da Ruhun naka (naka)
Kai ne mai badda rai ai Sakarmenti