Na Zo In Yi Maka Godiya by Solomon Odo — Lyrics

Solomon Odo Hausa Offertory Hymns Gospel Acclamation / Alleluia Hymns Solfa notation

Full Lyrics

[CHORUS] Allah na, na zo in yi maka godiya. Allah na, na zo in gode maka domin abinda ka yi mani. Na zo in ce maka, Allah na gode. Ka bani rai, Allah ka bani lafiyan jiki. Allah na zo, karɓi godiya ta. [VERSE 1] Na tashi daga barci da safe, na buɗe idanu na, albarkun ka Allah, albarkun ka na gani. Waɗansu ba su tashi ba amma na tashi, shi ya sa na zo domin in yi maka godiya. [VERSE 2] Na yi tafiya zuwa wurare, Ka kai ni lafiya, ka dawo da ni lafiya, ka bani iko kan hanya, na kuma ci nasara. Domin haka na zo in yi maka godiya. Na zo da farin ciki da wakokin yabo. [VERSE 3] Ka ciyar da ni, ka suturar da ni. Abinda mutum bai yi ba ai kai Allah ka yi. Ka bani yara mata da maza. Ɗaukaka da girma duk naka ne. Shi ya sa na zo domin in yi maka godiya. [ALLELUIA] Alleluia, Alleluia, Alleluia, Alleluia. Alleluia, Alleluia.

Download the sheet music

Na Zo In Yi Maka Godiya

Na Zo In Yi Maka Godiya

By Solomon Odo
Solfa
Hausa
3 pages
4 Downloads
Offertory Hymns Gospel Acclamation / Alleluia Hymns Uncategorized
0 0

More lyrics you may want