Full Lyrics
CHORUS
Ku ci, ku sha.
Jikin Sa abinci ne.
Shi ya ba mu da ran Sa domin mu sami ceto.
Sabuwar alkawari ta sabuwar hanya.
VERSE 1
Abinci ne mai dadi, abinci ne mai kyau,
Wanda Yesu ya ba wa duniya,
Don watan wata rana mu nuna wa yan uwa.
VERSE 2
Idan mun ci burodi, mun sha calis na wain,
Jiki da Jini wanda shi Yesu ya ba wa duniya,
Don watan wata rana muma mu nuna wa yan uwa.
VERSE 3
Musa ido ga Yesu, wanda Uba ya aiko,
Domin mu sami wannan salama, ya ba wa duniya,
Don watan wata rana muma mu nuna wa yan uwa.
VERSE 4
Idan muna jin yunwa, idan fa muna kishirwa,
Ga abincin ruhu da shi Yesu ya ba wa duniya,
Don watan wata rana muma mu nuna wa yan uwa.
VERSE 5
Kuzo wurin Dan Allah, kuzo wurin mai rai,
Ga Bautin kiya wanda shi Allah ya ba wa duniya,
Don watan wata rana muma mu nuna wa yan uwa.