Full Lyrics
CHORUS
Ga Burodi da Wain zasu zama mana abincin Ceto,
Wanda Yesu ya koya mana mu mika masa don tunawa da Ceton duniya,
za su zama Jiki da Jinin Yesu abinci na kullum,
don gafatan zunubai domin tarayya a Sama.
Allah mun gode, karbi baikonmu a yau.
SOPRANO AND ALTO
1. Ya Ubangiji karbi hadaya na Burodi da Wain da muka kawo,
ka tsarkake ka sa albarka,
ka karfafa aniyar mu mu zama daya.
2. Wannan hadaya ta Missa ta sulhunta duniya da Sama,
ta kan ba mu Salama da bauta ta gaskiya.
Za ya karfafa mu a kai a kai.
3. Mun gode, Ubana Sama, mun gode Mahallicin mu.
TENOR
1. Ya Allah Mai kauna mara matuka.
2. Muna godiya, Mu na daukaka.
3. Mun zo gaban bagadi da Burodi da Wain
REFRAIN TUTTI
Mun gode Mahallicin mu.
Mun gode, Ubana Sama mun gode Mahallicin mu.