Full Lyrics
Jikin Yesu da dadi,
Jininsa da dadi,
wanda ya karba da zuciya mai tsabta
lallai hakika zai rayu da ni.
Zo mu karbi gurasan rai na matuka
domin mu rayu da Yesu Kristi har abada.
Ubangiji shine gaskiya,
shine hanya, shi ne rai,
ba mai zuwa wurin Uban sai ta wurinsa.
Cikin daren da aka bashe Yesu,
ya dauki burodi yayi godiya.
Ya ba almajiransa yana cewa,
karba dukanku ku ci.
Cikin daren da aka bashe Yesu,
ya dauki calis yayi godiya.
Ya ba almajiransa yana cewa,
karba dukanku ku sha.
Ku dinga yin haka domin tunawa da ni a ko yaushe.
Abinci na malaiku,
muje mu ci mu sami raina mara matuka.
Abinci na tsarkaku,
muje mu ci mu sami raina mara matuka.
Abincin 'ya'yan Allah,
muje mu ci mu sami raina mara matuka.
Kuzo mu, sai ku zo mu ci abincin
domin mu rayu har a karba,
ku zo mu karbi jikin Yesu mai Ceto
domin mu rayu da shi har abada.
Amin.