Full Lyrics
[Intro]
Daukaka cikin samaniya
[Gloria]
A duniya salama ga mutane nufi mai kyau.
Muna yabon ka,
Muna albarkacen ka.
Muna yin maka godiya saboda darajar ka mai girma.
Ya Ubangiji Allah Sarkin Sama,
Allah Uba mai iko duka.
Ya Ubangiji Yesu Kristo 'Da makadaici.
Ya Ubangiji Allah Dan tunkiya na Allah,
Ya Ubangiji Allah Dan Uba.
Kai da kake kawar da zunuban duniya,
Kayi mana jin kai, kayi mana jin kai.
Kai da kake kawar da zunuban duniya,
Ka ji addu'ar mu, addu'ar mu.
Kai da kake zaune a hannun dama na Allah,
Ka yi mana jin kai, kayi mana jin kai.
Domin kai kadai Mai tsarki ne,
Kai kadai Ubangiji ne,
Kai kadai madaukaki ne.
Ya Yesu Kristo,
Tare da Ruhu Mai Tsarki,
Cikin daraja Allah Uba.
Amin, Amin, Amin, Amin.