Daukaka Ga Allah by Jude Nnam — Lyrics

Jude Nnam Hausa Gloria Solfa notation

Full Lyrics

Daukaka ga Allah cikin samaniya, A duniya kuma salama ga mutane na nufi mai kyau. Muna yabon ka, mun'albarkacan ka, Muna yi maka sujada. Muna daukaka ka, muna yi maka godiya, Saboda darajar ka mai girma. Ubangiji, Ya Ubangiji Allah Sarkin sama, Allah Uba mai iko duka. Ya Ubangiji Yesu Kristo, Da maka dai. Ya Ubangiji Allah, Dan tunkiya na Allah, Dan Uba. Kai da kake kawar da zunuban duniya, ka yi mana jinkai. Kai da kake kawar da zunuban duniya, ka ji addu'armu. Kai da kake zaune a hannun dama na Uba, ka yi mana jinkai. Domin kai kadai Mai Tsarki ne, ya Yesu Kristo. Tare da Ruhu Mai Tsarki cikin darajar Allah Uba. Amin.

Download the sheet music

Daukaka Ga Allah

Daukaka Ga Allah

By Jude Nnam
Solfa
Hausa
2 pages
42 Downloads
Gloria
0 0

More lyrics you may want