Full Lyrics
Daukaka ga Allah cikin samaniya.
A duniya kuma, salama ga mutane masu nufi mai kyau.
Muna yabonka, muna albarkace ka,
muna yi maka sujada.
Muna daukaka ka, muna yi maka godiya,
saboda darajarka mai girma.
Ya Ubangiji Allah sarkin sama, Allah Uba mai iko duka.
Ya Ubangiji Yesu Kristo, Dan makadai.
Ya Ubangiji Allah, Dan tunkiya na Allah, Dan Uba.
Kai da kake kawar da zunuban duniya, ka yi mana jinkai.
Kai da kake kawar da zunuban duniya, karbi addu'armu.
Kai da kake zaune a daman Uba, ka yi mana jinkai.
Domin kai kadai mai tsarki ne, kai kadai Ya Yesu Kristo.
Tare da Ruhu Mai Tsarki cikin darajar Allah Uba. Amin.