Full Lyrics
REFRAIN
Daukaka ga Allah A cikin Samaniya
Daukaka ga Allah A cikin Samaniya Ya Allah Daukaka
Allah A cikin Samaniya
VERSE 1
A duniya kuma Salama ga mutane na nufi mai kyau
Muna yabon Ka muna albarkace Ka
Muna yi maka sujada muna daukakan Ka
Muna yi maka godiya saboda darajar Ka mai girma
Ya Ubangiji Allah Sarkin Sama
VERSE 2
Allah Uban Mai iko duka
Ya Ubangiji Yesu Almasihu
Muna yabon Ka Ya Ubangiji Allah
Dan tunkiya na Allah Dan Uba
VERSE 3
Kai da Ke Kawar da zunuban duniya ka yi mana jin Kai
Kai da Ke Kawar da zunuban duniya Ka yi addu'ar mu
Kai da Ke Zaune a hannun dama uba Ka yi mana jin kai
VERSE 4
Domin Kai Kadai Mai tsarki ne
Kai Kadai Ubangiji ne
Kai Kadai Mai daukaki ne Ya Yesu Almasihu
Tare da Ruhu Mai Tsarki cikin darajar Allah Uba Amin