Full Lyrics
REFRAIN
Daukaka ga Allah a cikin Sama,
Daukaka ga Allah a cikin Samaniya.
Daukaka ga Allah cikin Sama o.
VERSE 1
Daukaka ga Allah cikin Samaniya
a duniya salama ga mutane na nufi mai kyau
muna yabon ka, muna albarkace ka
muna yi maka sujada.
VERSE 2
Muna daukakar ka, muna yi maka godiya,
sabo da darajar ka mai girma.
Mai girma Ya Ubangiji Allah Sarkin Sama
Allah Uba Mai iko duka.
VERSE 3
Ya Ubangiji Yesu Kristo Dan Makadaci,
Ubangiji Allah Dan Tunkiya na Allah
Ya Ubangiji Allah Dan Uba
Kai da ke kawar da zunuban duniya.
VERSE 4
Ka yi mana jinkai, ka yi ka yi mana jinkai,
Kai da kake kawar da zunuban duniya.
Ka ji addu'ar mu, ka ji ka ji addu'ar mu.
Kai da kake zaune a hannun dama na Allah.
VERSE 5
Ka yi mana jinkai, Ka yi mana jinkai,
domin kai kadai Mai tsarki ne, kai kadai
kai kadai Ubangiji ne, kai kadai
Madaukaki ne. Yesu ya Yesu Kristo.
ENDING
Tare da Ruhu Mai tsarki cikin darajar Allah Uba.
Amin, Amin.