Full Lyrics
Daukaka cikin samaniya, o cikin samaniya,
A duniya salama ga mutane nufi mai kyau, daukaka cikin.
Muna yabon ka, muna albarkacen ka, daukaka cikin.
Muna yin maka godiya saboda darajar ka mai girma, daukaka cikin.
Ya Ubangiji Allah Sarkin Sama, daukaka cikin.
Allah Uba mai iko duka, daukaka cikin.
Ya Ubangiji Yesu Kristo Dan makadaici, daukaka cikin.
Ya Ubangiji Allah Dan tunkiya na Allah, daukaka cikin.
Ya Ubangiji Allah Dan Uba, daukaka cikin.
Kai da kake kawar da zunuban duniya, daukaka cikin.
Ka yi mana jinkai, ka yi mana jinkai, daukaka cikin.
Kai da kake kawar da zunuban duniya, daukaka cikin.
Ka ji addu'ar mu, ka ji addu'ar mu, daukaka cikin.
Kai da kake zaune a hannun dama na Allah, daukaka cikin.
Ka yi mana jinkai, ka yi mana jinkai, daukaka cikin.
Domin kai kadai Mai tsarki ne, daukaka cikin.
Kai kadai Ubangiji ne, daukaka cikin.
Kai kadai madaukaki ne, daukaka cikin.
Ya Yesu, Ya Yesu Kristo, daukaka cikin.
Tare da Ruhu Mai Tsarki, daukaka cikin.
Cikin darajar Allah Uba, daukaka cikin.
Amin, Amin, Amin, Amin, daukaka cikin.