Daukaka by Agba Ben Stephen — Lyrics

Agba Ben Stephen Hausa Gloria Hymns Mass Settings Staff & Solfa notation

Full Lyrics

[Chorus] Daukaka cikin samaniya. Daukaka cikin samaniya. [Verse 1] A duniya salama ga mutane nufi mai kyau. Muna yabon ka muna albarkace ka. Muna yi maka sujada muna daukaka ka. Muna yi maka godiya darajar mai girma. Ya Ubangiji, Allah Sarkin sama. Allah Uba, mai iko duka. [Verse 2] Ya Ubangiji Yesu Kristo Da makadaici. Ya Ubangiji Dan tunkiya na Allah. Ya Ubangiji, Allah Dan Uba. Kai da kake karba Da zunuban duniya. Ka yi mana jinkai, ka yi mana jinkai. Kai da kake karba, Da zunuban duniya. [Verse 3] Ka ji addu'ar mu, ka ji addu'ar mu. Kai da kake zaune a hannun dama na Uba. Ka yi mana jinkai, ka yi mana jinkai. Domin kai kadai mai tsarki ne. Kai kadai Ubangiji ne. Kai kadai Madaukaki ne. [Verse 4] Ya Yesu, Ya Yesu Kristo. Tare da Ruhu mai tsarki. Cikin darajar Allah Uba. Amin, amin, Amin.

Download the sheet music

Daukaka

Daukaka

By Agba Ben Stephen
Staff & Solfa
Hausa
2 pages
1 Downloads
Gloria Hymns Mass Settings
0 0

More lyrics you may want