Full Lyrics
CHORUS
Abincin Alheri, shi ne za mu ci.
Abincin Alheri daga wurin Allah Oh!
Abincin Alheri za mu ci.
VERSE 1
Yesu ya dauki gurasa ya ba mu
Ya ce wannan shi ne jikina da zan ba ma dukan mutane.
Kristi ya dauki koko ya ba mu
Ya ce wannan shi ne jinina da zan ba wa dukan mutane.
VERSE 2
Gurasa da kokon da mun karbi
Shi ne jikin, shi ne jini Yesu.
Duk wanda ya karbe shi a cikin tsarkakiya
Zuciyar zai samu rai har abada.
In kana kaunarsa, zai samu rai har abada.
VERSE 3
Ku zo ku karbi shi
Ku zo ku karbi shi masu bauta,
Yana da dadi,
Zai ba ku rai
Mai tsarki, mai kauna, mai jinkai, mai salama
Ku zo, ku karbi shi.