Full Lyrics
CHORUS
Ku zo mu karbi abinci mai dadi,
Wanda Yesu Kristi ya bamu domin mu rayu.
Ku zo mu je wurin wannan Dan tunkiya,
Na Allahn mu domin mu sami rai na har abada.
VERSE 1
Babu shakka,
Cikin Yesu abinci ne na ruhu da rai.
Jinin Yesu abin sha ne mai ba da rai.
Sai ku zo masu kishin Dan tunkyan Allahn mu,
Don lallai mu sami rai na har abada.
Wanda yaci jikin Yesu ya sha jininsa,
Zai rayu har abada lallai babu shakka.
VERSE 2
Ku zo mu je, ku zo mu je,
Mu karbi jikin Yesu don mu sami rai,
Madawami da abada ma,
Yau ku zo, ku zo mu je.