YA YESU GA NI NA ZO by Jerson Jedalah Gitik — Lyrics

Jerson Jedalah Gitik Hausa Lenten Hymns Prayer Hymns Offertory Hymns Solfa notation

Full Lyrics

VERSE 1 Ya Yesu ga ni na zo, da duk kowace kasawata; Domin neman gafarata wurin alherinka. Bayyana ikonka yau, don ka kone duk muguntata, sai ka cika ni da dukan ruhuwanka. VERSE 2 Karfina, iyawata, har ma duka adalcina; Duk sun kasa cikata bukatan shari'anka. Cikin alherinka ne, akwai cikakkiyar gafura; cikin ta kwa ake iya bin nufinka. VERSE 3 Girma da darajarka, duk ka bar su cikin Sama can, Har ka sauko duniyan nan duk domin cetonmu; Wahalar kan giciye da mut'war da ka yi domin na wannan kauna lallai babu misalinta. VERSE 4 Cikin mulkin sama can yabon nasaranka ake yi, Wannan nasara ita ce nasarata yau; Yabon ka zan rika yi cikin zuciyata, furci da aikata nufinka, daga yau har abada. CHORUS Sauko da Ruhunka yau, Ya Yesu Ubangijina. Bude mani zuc'yata; Ka nuna mani nufinka; Don in yi nasara da shaidan da duk jurabobin duniya; Cikin sunan Allah, Uba Madaukaki.

Download the sheet music

YA YESU GA NI NA ZO

YA YESU GA NI NA ZO

By Jerson Jedalah Gitik
Solfa
Hausa
1 page
1 Downloads
Lenten Hymns Prayer Hymns Offertory Hymns
0 0

More lyrics you may want