Ya Yesu Gani Na Zo by Jerison Jedaiah Gitiki — Lyrics

Jerison Jedaiah Gitiki Hausa Hymns Lenten Hymns Offertory Hymns Prayer Staff & Solfa notation

Full Lyrics

VERSE 1 Ya Yesu ga ni na zo, da duk kowace kasawa ta, domin neman gafara ta wurin alherinka. Bayana ikonka yau, don ka kone duk mugunta ta sai ka cika ni da dukan rayuwanka. VERSE 2 Karfina, iyawa ta, har ma duka da adalci na, duk sun kasa cika tabuka kan shari'anka. Cikin alherinka ne, akwai cikakkiyar gafara cikin ta kwa ake iya bin nufinka. VERSE 3 Girma da darajar ka, duk ka bar sa cikin sama can, har ka sauko duniyan nan duk domin cetonmu. Wahalar kan giciye, da mu warda kayi dominmun wannan kauna lallai babu misalinta. VERSE 4 Cikin mulkin sama can, yabon nasaranka ake yi, wannan na sarata a yau; Yabon ka zan rika yi, cikin tunani furci da aikata nufinka, daga yau har abada. REFRAIN Sauko da Ruhun ka yau, ya Yesu Ubangiji na. Bude mani zuc'ya taka nuna mini nufinka, don ni yi nasara da shaidan da duk jarabobin duniya cikin sunan Allah, Uba madaukaki.

Download the sheet music

Ya Yesu Gani Na Zo

Ya Yesu Gani Na Zo

By Jerison Jedaiah Gitiki
Staff & Solfa
Hausa
1 page
4 Downloads
Hymns Lenten Hymns Offertory Hymns Prayer
0 0

More lyrics you may want