Full Lyrics
VERSE 1
Allah saboda rashin bin umurnin ka
Rayuwan dun'ya nan tayi mana wuya
Ba zamu iya in ba tare da kai ba
Kaji tausayin mu.
VERSE 2
Allah mai jinkai kaji tausayin mu
Wahalolin duniya sunfi karfin mu
Ya'yan ka sun kasa ga darajar ka
Kaji tausayin mu.
VERSE 3
Allah mai jinkai kaji tausayin mu
Yake yake ko ina babu salama
Mun gane kasawan mu Allah gamu mun zo
Kaji tausayin mu.
VERSE 4
Kaunar ka ya Allah babu iyaka
Alherin ka yafi gagara misali
Karka yashe mu Allah mai jintausayi
Kaji tausayin mu.