Godiya by Omachi Atome Michael — Lyrics

Omachi Atome Michael Hausa Offertory Hymns Hymns Celebrations Solfa notation

Full Lyrics

CHORUS Godiya muna godiya mun kawo godiya gare, a gare ka yau muna godiya muna miƙa godiya ka karbi godiya wanda muka kawo, muna farin ciki farin ciki da yabo, da girma muna ɗaukaka ka don alherin ka. Allah mun gode, mun gode, mun gode, Allah mun gode, mun gode, mun gode. VERSE 1 Godiya ya dace ga Allah ai, shi, ya bamu nasara shi ya bamu kome. Mu nuna godiya, godiya, godiya ga Allah, a kwanakin mu, a kullayaumi, raira, Ubangiji mai tsarki ne. VERSE 2 Rayuwa sai da ikon Allah, sai da kyautar Allah, Allah, Allah, Allah mai rufan asiri, Allah Sarkin Runduna, Shi kadai ya isa yabo. VERSE 3 Godiya daga zuciya, godiya daga zuciya, muka kawo wa Allahnmu. Godiya, mun kawo godiya, mun kawo godiya daga zuciya, mun kawo godiya ga Allah Uba, da Ɗa, da Ruhu mai Tsarki, Allah ɗaya Mai Tsarki, mun kawo godiya, mun kawo godiya da kiɗe kiɗe da kayan rawa muna taka rawa da farin ciki muna gode wa Allah, Allah sarkin, Sarkin Runduna.

Download the sheet music

Godiya

Godiya

By Omachi Atome Michael
Solfa
Hausa
4 pages
3 Downloads
Offertory Hymns Hymns Celebrations
0 0

More lyrics you may want